BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da daya
Shin yin guda ya halatta?
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam ina so a yi min bayani game da auren mace kirista a Musulunci. Ko ana iya yi a wannan lokacin?
Daga Abdullahi Ib Umar Doma jihar Nassarawa
SHAIKH ZAKZAKY: To ko a wane lokaci ma ba a yi, ballantana wannan. In dai aure ne, musulmi lazim ne ya auri Musulma, kamar yadda yake ita ma musulma lazim ne ta auri musulmi. Sai dai akwai masu cewa aure Munkadi'i yana iya halasta da Bakitabiya hasatan koma bayan sauran nau'o'in kafirai.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam ni dai ina tunatarwa ne a masallacin Juma'ar garin da nake, kuma idan ina tunatarwar, jama'a kan miko sadaka, duk da cewa ba ni na roke su ba. Shin ko ya halasta na yi amfani da wannan sadakar da jama'a ke ba ni?
Daga Abu Musa Geidam jihar Yobe.
SHAIKH ZAKZAKY: Tunda dai sadaka suka ba ka, za mu iya cewa ya halasta. Sai dai tun da dai wa'azi kake yi, abin da ya fi kamata shi ne ka nuna masu cewa, a daidai lokacin da kake wa'azin nan, kai dai a saurari wa'azin ne kawai, a daina ba ka sadakoki don kada yau da kullun ya zama kuma ranar da ka yi wa'azin babu sadakar, ka ji wa'azin bai wa'azantu ba sosai, har wata rana ya zama salon wa'azin naka ya sake. Kodayake wannan za a yi la'akari da ganin mutane da wannan. Tunda akwai wani wurin da wasu ba'adin 'yan uwa suka je wa'azi, sai suka hana a kawo sadaka din. Su kuma mutanen sai suka dauki abin yana nufin wani abu ne daban, don su a fahimtarsu haka dama ake yi.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, nine Yayana ya rasu ya bar min marayu kanana ina kulawa da su, amma kuma ina zaune ne a gidan nasu, menene matsayin zamana a gidan? Zan rika biyan haya ne ko kuwa zama ya halatta gare ni ba tare da na biya ko sisin kwabo ba?
Daga Shehu Hukuma Makuwanna Sabon Gobir jihar Sakkwato
SHAIKH ZAKZAKY: Za mu kalli abin ta fuska biyu, idan kai an dauke ka aiki ne ka kula da marayu, kuma daga cikin sharuddan aikin har da cewa za ka zauna a nan ne ka kula da su, to ka ga kai ma'aikacin kula da Marayu kenan. Idan kai ne ka dauki Marayun kake lura da su, ka ga ai a gidanka kenan. Saboda haka ka ga suna da hakki a nasu gidan.
TAMBAYA: Akramakallah, mace ce mijinta ya bar gida yau shekaru biyu, tun ana jin labarinsa yanzu ba a ji, shin ko yaya za ta yi da auren nata?
Daga Musa Alhasan Unguwar Mu'azu, Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Sai ta kai kara wajen Hakimusshar'i wanda zai sa a bincika Nahiyoyin gabas da yamma, kudu da arewa. Har idan aka sami shekara hudu daga lokacin da ta kai karar, ba daga lokacin da ya bar gida ba. Daga lokacin da ta kai karar har aka sami shekara hudu cur ba ji labarinsa ba;to sai shi Hakimusshar'i ya ba ta daman ta fara idda. Idan ta kammala iddarta mijin bai dawo ba, to ta samu ta yi aure. Idan kuma ya dawo tana idda, to shi kenan aurensu na nan. In kuma ya dawo bayan ta gama idda, sai dai a sake daura auren.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, mutum ne ya nemi aikin gwamnati. Bayan an ba shi takardar kama aiki, sai wanda zai ba shi takardar ya ce sai ya ba shi wani abu, to ko ya halatta in ba shi?
Daga Hadi Ayuba 'Yankara jaula32@yahoo.com.au
SHAIKH ZAKZAKY: Abin da za mu kwatanta da wannan shi ne kamar fatawar Imam a kan idan mutum yana bidar aure, waliyyin matar ya gindaya masa wani sharadi na cewa sai ya ba shi wani abu kafin a ba shi auren, ya ce ya halasta ya bayar. Sai dai ya ce ya haramta ga shi wanda ya bidi ya ba shi din. To shigen haka nan ne wannan. In ya zama shi zai cutu in bai yi aikin ba, ya zama kuma ba yadda zai yi ya sami akin nan sai ya ba shi wani abu, to sai ya ba shi ya sami aikin. Bai da laifi a kan ba shi. Amma shi wancan, bai halatta masa ba in ya ci, wato ya ci haramun. Ka ga wato tamkar kwace kenan tunda an tilasta masa ne.
TAMBAYA: Menene hukuncin halartar taron yinin biki da matan aure ke yi? Shin ya halatta dan uwa ya bar matarsa ta halarci wannan bikin, ko kuma idan matarsa ta haihu ya bari a yi, duk da cewa idan ya yi shi a matsayin walima, idan matan suka taru za su iya mayar da shi kamar yadda suka saba, saboda al'adar garin, wato su sa kaset-kaset na kida suna rawa?
Daga Sanusi Lawwali, Finance Dept Anka LG, jihar Zamfara.
SHAIKH ZAKZAKY: Shi ma ya yi magana kan walima wadda ita shari'a ta san da shi. Saboda haka in dai walina ce ita sananniya ce, a kan tara mutane su ci abinci. Abin da ya kamata lazim ya kiyaye shi ne ya tabbatar da cewa abin da duk za a yi bai saba ma shari'a ba. Amma ba zai iya cewa shi ya tashi a walima ba. Walima ce, amma a kiyaye dole abin da za a yi bai saba ma shari'a ba. In ya saba ma shari'a, shi wannan abin da ya saba ma shiri'a din shi ne ya haramta, ba walimar ba.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Menene matsayin guda a Musulunci idan an samu wani abin farin ciki?
SHAIKH ZAKZAKY: Wannan dai al'adar mutane ne, ita kuma shari'a, in dai wani abu ba a hana ka ba, to shike nan kana iya yi kenan. Ba mu san inda aka ce a yi guda ba. Sai dai idan ya zamana akwai tabarruji na murya da zubar da daraja, to sai dai ta shiga ta wannan babi din. Amma abin sani bisa al'ada dama wadansu mutane ne kebantattu wadanda yake su a a wurinsu yin wannan abin tamkar wani abu ne wanda ake ganin bai zama zubar da mutunci ba, kila ma ya zama ado, kamar maroka ko abin da ya yi kama da haka. Ala ayyi halin dai, kamar yadda na fadi ne, in yana bukatar ya ji an ce an sami riwayar ne an ce a yi gudar, sai mu ce to ba mu san wannan ba. Amma duk abin da ba a hana ka ba, ya hallata maka ka yi. Sai dai idan kinsa ya zo ta wani babi daban.
TAMBAYA: Akramakallah. Ko ana iya amfani da duk wani irin kayan kide-kide da bushe-bushe wajen yin waken addini?
Daga Maina Mustafa, Malam Fatori, Abadam LG, jihar Borno.
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba za mu iya cewa haka nan ba, domin akwai wadansu kayan kade-kade da bushe-bushe wadanda suka shafi abin da za a ce ma lahawu. Idan ma'abota wargi sun kebanta da shi, kamar misali idan aka ce wani nau'in kida, dama ainihin na 'yan caca ne, masalan, ko kuma wani irin busa dama na mashaya ne, ko abin da ya ya yi kama da haka nan, to ba zai yiwu a dau shi irin wannan 'ala' din wanda aka san ma'abota wargi na amfani da shi a kawo shi cikin addini ba. In ka yi haka zai zama haramcinsa ma ya fi tsanani, in aka yi da sigar addini aka yi. Wato idan kade-kade da bushe-bushen da suka haramta, idan aka yi su da sigar addini, to haramcin ya fi tsanani. Saboda haka azabar da za a yi wa mai wannan, zai fi tsanani a kan ma ya je ya yi a gidan busa. Alal misali idan kidan da aka sani na gidajen shaye-shaye ne, sai wani ya dauke shi ya je da shi a masallaci ko a taron addini, to laifinsa zai fi na wanda ya yi shi a gidan shaye-shaye, tunda ya dace da gidan shaye-shaye ne. Wato a takaice kenan in an san wata 'ala' ta kida ta kebnta da ma'abota lahawu, to kar a yi amfani da wannan wajen addini.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ana bin sa bashin salloli masu yawa, shin zai iya yin sallar tahajjud ko kuma nafila kowace iri?
SHAIKH ZAKZAKY: Eh haka ne, idan mutum ana bin sa bashin sallar farali yana iya yin nafila, wannan haka yake dangane da salla. Na san mun sha amsa wannan. Cewa azumi ne, ba a yarda ana bin ka bashin azumi ka yi nafila ba, ko ka yi kuma bai inganta ba.